Sai dai Malam Inuwa Kubo ya yi bayanin cewa sai makarantun da suke a wuraren da aka tabbatar da tsaron su ne kadai za'a fara budewa tukunna.
Ya bayyana cewa, ayyukan ta'addanci da kungiyar Boko Haram ta yi sun yi mummunan wargaza tsarin karatu a jihar, ya kuma mika ta'aziyar shi ga shugabannin makarantun da suka rasa malaman su da 'yan uwa a sanadiyar wannan tashin hankali.
Kwamishinan ilimin ya ce daliban dake zuwa jeka ka dawo za'a basu abincin safe da na rana a makarantar a wani matakin da gwamnatin ta dauka don ba su kwarin gwiwwar dawowa makaranta.
Daga nan sai ya yi kira ga shugabannin makarantu da su dauki kiyasin kayayyakin karatu da kujeru da suka lalace a makarantun su sannan su mika shi ga hukuma don daukan mataki. Har ila yau ya kuma umurci dukkan shugabannin makarantun da su shirya sunayen malamai, dalibai da sauran mutanen da aka hallaka lokacin wannan masifar ta Boko Haram don a mika ma asusun gwamnatin tarayya na taimakama wadanda harin ya rutsa da su. (Fatimah)