Wata sanarwar da kakakin rundunar kanar Sani Kukasheka ya sanyawa hannu, ta ce cikin wadanda aka kubutar yayin farmakin na ranar Talata akwai yara kanana 192, da mata 138, da kuma wasu maza su 8. Tuni kuma aka garzaya da wadanda aka kubutar zuwa birnin Mubin jihar Adamawa.
Kazalika sanarwar ta tabbatar da hallaka mayakan kungiyar su 30, tare da kwace makamai da kayan fada da dama daga mayakan na Boko Haram.
A watan Agustar da ta gabata ne dai shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari, ya umarci dakarun sojin kasar da su kawo karshen kungiyar Boko Haran kafin karshen watan Disamba dake tafe, sai dai mutane da dama na bayyana shakku game da yiwuwar hakan, ganin yadda a baya bayan nan mayakan ke dada kaimin kai hare-haren kunar bakin wake a sasssan kasar daban daban. (Saminu Hassan)