Fiye da mahalarta dubu 300 da suka fito daga dukkan fadin duniya suka isa wannan babbar haduwa ta shekara, da za ta ci gaba da gudana har zuwa ranar 15 ga watan Nuwamba. Wani adadin 'yan kasuwa dake gudanar da harkoki ta intanet na tsakanin kasa da kasa, sun halarci wannan baje kolin a karon farko, inda suke gabatar da ayyukansu na kasuwanci, haka kuma tare da zummar neman fadada harkokin kasuwanci a birnin Lagos na wannan kasa. He Xiyang, wani mai gabatar da kayayyaki, kuma darektan Steelite Nigeria Limited, wani kamfanin dake hedkwata a jihar Ogun dake kudu maso yammacin Najeriya, ya bayyana cewa wannan baje koli wata babbar dama ce ga kamfaninsa na gabatar da sabbin kayayyakin da ya kera. (Maman Ada)