in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da takwaran sa na kasar Rasha
2014-07-15 10:19:32 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping da zai halarci taron shugabannin kasashe membobin BRICS karo na 6 ya gana da takwaran aikinsa na kasar Rasha Vlładimir Putin a ranar litinin 14 ga wata a birnin Fortaleza dake kasar Brazil.

A yayin ganawar, Xi Jinping ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen Sin da Rasha su ci gaba da goyon bayan juna a fannin siyasa, da kara yin hadin gwiwa wajen nazari da kuma habaka kan wasu muhimman ayyuka bisa manyan tsare-tsare, kana da gudanar da ayyukan hadin kai ta fuskokin aikin soja, kiyaye tsaro, da dai sauransu. Ban da wannan kuma, ya kamata kasashen biyu su nuna goyon baya wajen kafa makarantu da kuma raya al'adu tare. Ya ce yana fatan kasashen biyu za su kara daukar matakai bai daya kan harkokin kasa da kasa, da inganta hadin gwiwa dake tsakanin kasashe membobin BRICS, tabbatar da ikon yin magana da matsayinsu, da sa kaimi ga samun demokuradiyya kan dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, da kuma samun zaman lafiya da bunkasuwa a duniya baki daya.

A nasa bangaren, Shugaba Putin ya bayyana cewa, ya kamata a fadada cinikayya da zuba jari a tsakanin kasashen biyu, da kara hadin gwiwa a fannonin makamashi, kimiyya da fasaha, nazarin sararin samaniya, ayyukan more rayuwa na sufuri, yin musayar kudi da dai sauransu. Kana yana fatan za a kaddamar da yin shawarwari kan yarjejeniyar gina bututun iskar gas a tsakanin Rasha da Sin cikin hanzari, da karfafa hadin gwiwa a kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, da kungiyar G20, da sa kaimi ga yin kwaskwarima kan asusun ba da lamuni na duniya, da kuma tabbatar da tsaro a kan yanar gizo. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China