Bayan aukuwar hare-haren, shugaban majalisar dokokin kasashen Turai, Martin Schulz ya ba da wata sanarwa, inda ya jaddada cewa, kasashen Turai za su hada kansu, domin yaki da ta'addanci, kuma za su cire dukkanin kungiyoyin ta'addanci daga nahiyar Turai, tare da gurfanar da 'yan ta'adda a gaban kotu.
Bayan abkuwar harin ta'addancin kuma, gwamnatin Faransa ta shelanta kara tsaurara matakan tsaro da bincike a cikin jiragen kasa da na sama dake shiga kasar, yayin da kuma 'yan sanda a birnin Paris suka yi kira ga mazauna birnin da su rage fita waje. An rufe makarantu a birnin, da kuma rufe hasumiyar Eiffel a lokacin. Ban da haka, gwamnatin Faransa ta riga ta kara karfin tabbatar da tsaro a ofisoshin jakadanci da cibiyoyin al'adu da makarantu na kasar da ke katare.
Sai kuma kwamitin yaki da ta'addanci na Rasha ya ba da sanarwar cewa, sassan tsaro na kasar sun shiga shirin ko ta kwana sakamakon sabuwar barazanar ta'addanci da kasar take fuskanta.
Gwamnatin Italiya kuma ta sanar da daga matakin tsaro zuwa mataki na biyu a jiya, inda ta bukaci rundunar soja ta musamman da ta kara kulawa da iyakokin kasa, musamman ma iyakar kasa tsakanin Italiya da Faransa.
Sakamakon barazanar ta'addanci, Jamus, Belgium, Hungary da sauran wasu kasashe ma sun kara karfin tabbatar da tsaro a kasashensu.(Fatima)