in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka za ta kara sojoji 1300 a Iraq
2014-12-20 17:13:11 cri
Hukumar tsaron kasar Amurka ta ce a watan Janairun dake tafe, Amurka za ta tura karin sojoji kimanin 1300 zuwa kasar Iraqi.

Kakakin hukumar tsaron kasa ta Amurka John Kirby ne ya bayyanawa taron maneman labaru hakan, yana mai cewa cikin watan Nuwanbar da ya gabata ne shugaba Barack Obama, ya amince da tura karin sojoji kimanin 1500 zuwa kasar ta Iraqi, kana sojojin su 1300 da za a tura nan da 'yan kwanaki, wani muhimmin mataki ne tabbatar da kudurin shugaba Obaman.

Mr. Kirby ya kuma jaddada cewa, za a girke tawagar sojojin na wannan karo ne a arewacin kasar ta Iraq, da kuma yankin Anbar dake yammacin kasar. Kana dakarun sojin za su mai da hankali ne ga ba da shawarwari, da kuma taimakawa sojojin tsaron Iraqin da dakarun Kurdawa wajen yaki da kungiyar IS a yankin, kuma sojojin ba za su shiga yaki kai tsaye ba.

Har wa yau sojojin za su rika ba da horo ga sojojin kasar ta Iraqi. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China