Wani jami'in tsaro na lardin Al-Anbar ya ce, a wannan rana, a birnin Fallujah da ke da nisan kilomita 50 yamma da birnin Bagadaza, kungiyar IS ta tura 'yan kunar-baki-wake da su je su ta da bom yayin da suke kusantar sojojin Iraqi, kuma hakan ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji 10, tare da jikkatar wasu 8. Kawancen sojoji da ke karkashin shugabancin Amurka sun tura jiragen saman yaki don jefa boma-bomai ga birnin Fallujah wato inda dakarun suka mamaye, abun da ya haddasa mutuwar dakarun IS a kalla 7, tare da jikkatar wasu 11.
Wannan jami'i ya ce, a wannan rana, sojojin Iraqi sun gwabza fada da dakarun kungiyar IS a yankin karkarar birnin Ramadi, hedkwatar lardin Al-Anbar, kuma abun da ya yi sanadiyyar mutuwar dakarun kungiyar IS a kalla 3, amma bai fayyace yawan sojojin da suka rasu ba.
Wani jami'in lardin Salahudin dake yankin arewacin kasar Iraqi ya bayyana cewa, a wannan rana, sojojin Iraqi sun dauki matakan soji a wuraren da ke kusa da birnin Tikriti wato hedkwatar lardin, sun kuma mamaye kauyuka guda 2 dake arewa da birnin Tikriti, inda aka harbe dakarun IS a kalla 3.(Bako)