Akwai manemi labari da ya tambayi Mr. Hong Lei cewa, bisa labarum da aka bayar, an ce, a ran 13 ga wata da dare, an haddasa jerin hare-haren ta'addanci a garin birnin Paris. Sakamakon haka, shugaba Francois Hollande ya shelanta kafa dokar ta baci a duk fadin kasar Faransa da rufe kan iyakar kasa da kasa, ta yadda za a iya yin hadin gwiwa wajen yakar ta'addanci. Ina ra'ayin kasar Sin game da wannan lamarin?
Mr. Hong Lei y aba da amsa cewa, wannan jerin hare-haren ta'addanci da aka aikata a birnin Paris, inda aka haddasa mutuwar dimbin mutane ya girgiza bangaren Sin kwarai. Saba da haka, kasar Sin ta yi allah wadai ga wannan jerin hare-hare, kuma ta juna ta'aziyya ga wadanda suka rasu a cikin lamarin, kuma ta nuna janjantowa ga iyalan wadanda suka rasu, da wadanda suka jakkata a cikin lamarin. Ta'addanci kalubale mai tsanani da dan Adama ke fuskanta tare, tabbas ne, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan matsayin nuna goyon bayan matakan yakar ta'addanci da gwamnatin kasar Faransa ta dauka domin tabbatar da kwanciyar hankalin kasar. (Sanusi Chen)