in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan majalissun dokokin Afrika suna ingiza amincewa da dokar yanayi a Paris
2015-11-12 13:29:14 cri
'Yan majalissun dokokin kasashen dake kudu da Hamadar Sahara a ranar laraban nan suka yanke shawarar neman goyon bayan sauran kasashen duniya domin amincewa da sabuwar doka da za ta hana a fitar da iskar gas din da zai gurbata yanayi.

'Yan majalissun wadanda suka hadu a taron da aka yi a birnin Nairobin kasar Kenya sun yanke shawarar ne baki daya da zai bukaci hukumomin daban daban da masana'antu da ma kungiyoyin jama'a da su goyi bayan hakan bisa dokar da za ta samar da dokar yanayi.

A cikin jawabin shi na bude taron, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya jaddada cewa sabon dokar yanayin yana da muhimmanci ma Afrika don ya basu damar sabawa da yadda ake ganin hakan ke kawo faruwar fari, ambaliya da barkewar cututtuka.

A lokacin taron 'yan majalissun za su duba yadda za su yi amfani da wannan lokaci su canza bangarorin samar da sabbin hanyoyin makamashi ta hanyar dokokin, cigaba da wanzuwa da kuma tantance shi kwarai.

'Yan majalissun daga kasashen Kamaru, Kenya, Najeriya,Namibiya, Saliyo, Zambiya da kasar Birtaniya zasu karu daga juna tare da amfanin da bayanin a kan misalan nasarar da kowannen su ya samu da kuma matakan da aka dauka game da makamashi da cigaba mai dorewa, inda aka gayyato kwararru daga cikin al'ummomi, kungiyoyin jama'a da na kasashen waje.

Shugabannin siyasar na Afrika, 'yan majalissun dokoki da masu fafutukar kare muhalli sun hade wajen daya don neman a samar da doka cikin adalci da daidaito da zai taimaka ya daidaita yanayin na duniya.

Shugaba Kenyatta ya ce Shugabannin kasashen Afrika da zasu halarci taron birin Paris za su nemi goyon bayan na samun Karin kudade , canza fasaha, kara gina dabaru don inganta kokarin nahiyar ta fuskanar sauyin yanayi.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China