in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka tana begen ziyarar da shugaban Sin zai kai kasar
2015-09-18 14:48:42 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka John Kirby ya bayyana cewa, Amurka tana begen ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai kasar. Amurka tana farin ciki sosai da wannan ziyara.

Kirby ya bayyana a shaidawa taron manema labaru cewa, dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka tana da muhimmanci sosai. A yayin da tattalin arzikin kasar Sin ke kara bunkasa, kuma kasar ke kara taka muhimmiyar rawa a duniya, dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka za ta kara yin tasiri ga yankin Pasifik har ma ga duniya gaba daya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China