in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta harbe tauraron dan Adam mai lamba 28 domin gano abubuwan dake nesa
2015-11-08 17:07:46 cri
Da misalin karfe 3 na yammacin ranar 8 ga wata ne, kasar Sin ta cimma nasarar harbe tauraron dan Adam mai lamba 28 domin gano abubuwan dake nesa ta hanyar rokar dake dauke da kumbon dan Adam na Changzheng lamba na 4 a cibiyar harbe tauraron dan Adam dake birnin Taiyuan na kasar Sin.

Cibiyar nazarin sararin samaniya ta kasar Sin ta sarrafa tauraron dan Adam din da aka harbe a wannan karo, wanda za a yi amfani da shi a fannonin kimiyya da fasaha, yin bincike albarkatun kasa da gonaki da kuma yin rigakafi kan bala'u da dai sauransu.

Haka kuma, wannan shi ne karo na 217 da rokar mai dauke da tauraron dan Adam ta Changzheng ta gudanar da aikin harbe tauraron dan Adam cikin nasara.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China