in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta samu nasarar harba wani tauraron dan Adama na sadarwa
2015-10-17 12:42:38 cri
Da misalin karfe 12 da minti 16 na tsakan daren ranar Asabar 17 ga wata, kasar Sin ta yi amfani da rokar daukar kaya mai suna Dogon Zango mai lambar 3B ta harba wani tauraron dan Adama ta sadarwa kirar Asiya-Pasifik mai lamba 9 a filin harba tauraron dan Adama na yankin Xichang dake arewa maso yammacin kasar. Wannan ne karo na farko da kasar Sin ta ba da hidimar harba tauraron dan Adama na sadarwa ga kamfanin sadarwa wanda ya dade yana aiki da taurarin dan Adama na sadarwa.

Shi ne kuma karo na farko da kamfanin Asiya-Pasifik na Hongkong mai aiki da taurarin dan Adam na sadarwa ya sayi tauraron dan Adam na sadarwa na jama'a da babban yankin kasar Sin ya kera domin kasuwa. Bisa shirin da aka zana, wa'adin aiki na wannan tauraron dan Adama din da ke da na'urorin mika alamun sadarwa mafi yawa zai kai tsawon shekaru 15. Bayan ya shiga hanyarsa a can sararin sama, yawan mutanen da zai shafa a yankunan Asiya, Turai, Afirka da Australiya zai kai kashi 75 cikin dari. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China