A yammacin ranar 13 ga wata ne aka yi bikin bude cibiyar kula da tsarin zirga-zirga ta hanyar tauraron dan Adam mai suna "Beidou" ta birnin Zhongshan dake lardin Guangdong a kudancin birnin Zhongshan, inda Shen Rongjun ya yi bayani cewa, an samun babban ci gaba kan tsarin na Beidou a wadannan shekaru biyu, inda aka samar da na'urorin da suka dace da wannan tsari, koda ya ke ana bukatar a kara inganta kayayyakin fasahohin zamani da za su dace da tsarin.
Shen Rongjun ya kara da cewa, yanzu tsarin Beidou ba zai maye gurbin tsarin GPS ba. Duk da cewa ana gudanar da wadannan tsare-tsare biyu tare, ana iya yin amfani da tsarin GPS ko a'a,amma idan ana bukatar gudanar da ayyuka yadda ya kamata, ya fi kyau a amfan da tsare-tsaren guda biyu tare. (Zainab)