in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi nasarar harba tauraron dan Adam mai suna "Chuangxin 1-04"
2014-09-04 15:29:58 cri
A ranar 4 ga wata da karfe 8 da minti 15 na safe a cibiyar harba tauraron dan Adam ta Jiuquan da ke lardin Gansu a arewa maso yammacin kasar Sin, kasar ta Sin ta yi nasarar harba tauraron dan Adam mai suna "Chuangxin 1-04" ta hanyar amfani da roka samfurin "Changzheng 2-4", kuma tauraron dan adam din ya shiga hanyarsa kamar yadda aka tsara, yayin da rokan ya kuma dauki wani tauraron dan Adam na gwaji da ya shafi harkokin sadarwa.

Tauraron dan Adam din mai suna "Chuangxin 1-04"wanda kwalejin nazarin harkokin kimiyya na kasar Sin ya kera, za a yi amfani da shi ne wajen tattara bayanai daga tashoshin sa-ido da suka shafi adana ruwa, yanayi, wutar lantarki, yaki da bala'u da dai sauransu. Kuma za a yi amfani da tauraron dan Adam na gwaji na sadarwa don yin gwajin aikin sadarwa ta hanyar tauraron dan Adam. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China