Mr. Wang ya bayyana hakan ne yayin zantawa da takwaransa na kasar Amurka John Kerry ta wayar tarho bisa gayyatar da aka yi masa. Wang Yi ya ce, biyowa bayan ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai kasar Amurka cikin cikakkiyar nasara, dangantakar kasashen biyu na fuskantar babbar dama. Don haka ya kamata Sin da Amurka su inganta shawarwari tsakaninsu, don daukar matakai a fannonin da shugabannin kasashen biyu suka cimma matsaya a kan su, da tabbatar da raya dangantakar kasashen biyu. Kaza lika ya kore fatan kawo cikas game da wannan yunkuri.
Wang Yi ya ce, Sin na dora muhimmanci ainun game da wannan batu. Kuma ya kamata Amurka ta gaggauta komawa hanyar shawarwari domin kaiwa ga warware rikici a tsakanin sassan biyu.(Bako)