Dangane da lamarin, majalisar gudanarwar kasa ta Amurka ta fidda wata sanarwar da ta nuna maraba da ganawar shugabannin biyu, a sa'i daya kuma, tana maraba da babban ci gaban da aka samu kan dangantakar bangarorin biyu.
Kana, ma'aikatar harkokin wajen kasar Faransa ta fidda wata sanarwa cewa, ganawar tsakanin shugabanni Xi Jinping da Ma Ying-Jeou za ta ciyar da zaman lafiya, shawarwari da hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu gaba.
Haka kuma, kakakin hukumar harkokin wajen kungiyar EU ya bayyana cewa, ganawar shugabannin bangarorin biyu ta kasance wani babban ci gaban da aka samu.
Ban da haka kuma, al'ummomin kasa da kasa na yaba wa ganawar shugabannin biyu sosai, ana kuma ganin cewa, lamarin na dauke da babbar ma'ana cikin tarihi, ana da imani cewa, za ta ciyar da dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu gaba, da kuma ba da gudummawa wajen cimma zaman lafiya da zaman karko cikin kasa da kasa. (Maryam)