Mr. Xi Jinping ya nuna cewa, yau rana ce ta musamman. Shugabannin bangarorin biyu na mashigin tekun Taiwan sun gana da juna, wannan zai zama wani sabon babi na tarihin huldar dangantakar dake tsakanin mashigin tekun Taiwan. Ba za a manta da wannan rana ba a nan gaba.
Game da batun bunkasa huldar dangantaka tsakanin bangarorin biyu na mashigin tekun Taiwan, Mr. Xi Jinping ya gabatar da ra'ayoyi hudu, wato, da farko dai, ya kamata a tsaya tsayin daka kan matsayin bin babbar ka'idar siyasa da bangarorin biyu suka cimma tare. Sannan, ya kamata a karfafa tushen bunkasa huldar dangantaka tsakanin bangarorin biyu cikin lumana. Na uku shi ne, ya kamata a tsaya kan matsayin neman samun alheri ga 'yan uwan bangarorin biyu baki daya. Na huku, ya kamata a yi kokarin farfadowar duk al'ummar Sinawa cikin zuciya daya.
Sannan, bangarorin biyu sun amince da muhimman sakamakon da bangarorin biyu suka samu bayan shekarar ta 2008. Dukkansu sun bayyana cewa, ya kamata a ci gaba da tsayawa kan ka'idar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya da bangarorin biyu suka amince a shekarar 1992, da karfafa tushen siyasa da suke zaune tare, ta yadda za a iya kara ciyar da dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu gaba cikin lumana da tabbatar da kwanciyar hankali a yankin mashigin tekun Taiwan. (Sanusi Chen)