in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Sin, Japan da Koriya ta kudu sun lashi takwabin zurfafa hadin gwiwa kan wasu batutuwa
2015-11-02 09:41:39 cri

Kasashen Sin, Japan da Koriya ta kudu sun amince su zurfafa hadin gwiwa a fannonin zirin Koriya da yadda za a hade tsarin tattalin arzikin yankin gabashin Asiya wajen guda.

Firaministan kasar Sin Li Keqiang da takwaransa na Japan Shinzo Abe da kuma shugabar kasar Koriya ta kudu Park Geun-hye ne suka bayyana haka cikin wata sanarwar bayan taron kolin da shugabannin suka gudanar a birnin Seoul. Shugabannin sun kuma jaddada muhimmancin karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen uku ta yadda za su bunkasa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Bugu da kari, kasashen uku sun sake nanata kudurinsu na nuna adawa da kera makaman nukiliya ko wani mataki da zai haifar da zaman dar-dar ko kuma keta kudurorin kwamitin sulhu na MDD a zirin na Koriya.

A cikin sanarwar, kasashen na Sin, Japan da kuma Koriya ta kudun sun amince su rika sanya ido don kawo karshen ayyukan masu satar bayanai ta Intanet, ayyukan ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi, kana za su hada karfi wajen ganin an inganta tsaron nukiliya.

Shugabannin kasashen na fatan yarjejeniyoyin da suka cimma za su kai ga cimma kyakkyawan sakamako kan hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen na Koriya.

A ranar Lahadin da ta gabata ne kasashen uku suka sake farfado da wannan taro bayan dakatar da shi da aka yi na kusan sama da shekaru uku. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China