in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya gana da shugaban majalisar dokokin kasar Korea ta Kudu
2015-11-01 17:40:30 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da shugaban majalisar dokokin kasar Korea ta Kudu Chung Ui-hwa a safiyar yau Lahadi 1 ga wata a birnin Seoul, hedkwatar kasar Korea ta Kudu.

Yayin ganawar tasu, Mista Li ya bayyana cewa, ziyararsa a wannan karo na da zummar kara inganta dangantakar sada zumunci tsakanin kasashen biyu, da inganta aminci tsakaninsu, da habaka mu'ammala, sannan da kara hadin gwiwa ta fuskar kirkire-kirkire, ta yadda za a kara bunkasa dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabon mataki.

A nasa bangare, Mista Chung Ui-Hwa ya ce, Sin da Korea ta Kudu na da zumunci na dogon tarihi, Korea ta Kudu na fatan kara dankon zumuncin kasashen biyu, tare da kafa kyakkywar makwabta da abokantaka a tsakaninsu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China