in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ganawa tsakanin manyan jami'an kasashen Sin da Korea ta Kudu
2015-11-01 13:43:16 cri

 

Firaministan kasar Sin Mista Li Keqiang ya gana da shugabar kasar Korea ta Kudu Madam Park Geun-hye a yammancin jiya 31 ga watan Oktoba a fadar shugaban kasar Korea ta Kudu ta Chong Wa Dae.

Yayin ganawar, Mista Li ya isar da gaisuwar shugaba Xi Jinping ga shugabar Park Geun-hye, inda ya kara da cewa, Sin na fatan kara hadin gwiwa da Korea ta Kudu a fannoni daban-daban, ta yadda za su samu bunkasuwa iri daban-daban.

A nata bangare kuma, Madam Park Geun-hye ta maraba da zuwan firaminista Li Keqiang, wanda shi ne karo na farko ya kai ziyara a kasar bayan ya zama firaminista. A cewarta, Korea ta Kudu na fatan kara hadin gwiwa da kasar Sin a fanonni daban-daban, ciki hadda ciniki, hada-hadar kudi, ayyukan kirkire-kirkire, kera kayayyaki, kiwon lafiya da dai sauransu, da kuma sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin kasashen biyu.

Yayin da suka tabo maganar halin da zirin Korea ke ciki, Mista Li ya ce, a halin yanzu kuma, ya kamata bangarori daban-daban su yi kokari tare don ci gaba da sa kaimi ga kawar da makaman nukiliya a zirin. Sin na tsayin tsaya daka kan kyautata dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu na zirin da kara azama kan samun sulhuntawa da hadin gwiwa a tsakaninsu.

Madam Park Geun-hye ta ce, kasarta na dora babban muhimmanci kan gudummawar da Sin ke bayarwa wajen kawar da makaman nukiliya a zirin Korea da tabbatar da zaman lafiya da karko a zirin, ita ma tana fatan kara yin mu'ammala da Sin kan batun zirin Korea, kuma Korea ta Kudu na fatan sa kaimi ga samun sulhuntawa da hadin gwiwa a tsakaninta Korea ta Arewa. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China