A jiya Litinin, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta shirya taron manema labaru kan ziyarar da firaministan kasar Li Keqiang zai kai zuwa Koriya ta kudu, da kuma halartar taron shugabanni karo na 6 tsakanin kasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu, inda mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Liu Zhenmin da mai taimakawa ministan ciniki Tong Daochi suka amsa tambayoyin manema labaru na kasar Sin da na kasashen waje.
Game da ziyarar firaminista Li a Koriya ta Kudu, Liu Zhenmin ya bayyana cewa, a 'yan shekarun da suka wuce, hadin kai a fannoni daban daban a tsakanin kasashen Sin da Koriya ta kudu na samun saurin bunkasuwa. Kasashen biyu na kokarin kafa dangantakar abokantaka a fannonin neman samun ci gaba tare, da tabbatar da zaman lafiya da kuma farfado da tattalin arzikin nahiyar Asiya, da ma inganta cigaban kasashen duniya baki daya.
Ziyarar ta kasance ta farko da Li Keqiang zai yi a Koriya ta Kudu tun bayan darewar sa kujerar firaministan, kuma ita ce ziyara ta biyu da wani firaministan kasar Sin zai yi a kasar cikin shekaru biyar, don haka ziyarar dai na da ma'ana kwarai waje karfafa dankon zumunta a tsakanin shugabannin kasashen Sin da Koriya ta Kudu, da inganta hadin kai a fannoni daban daban tsakanin bangarorin biyu, da kuma ciyar da dangantakar abokantaka tsakanin kasashen biyu gaba.
Game da taron shugabanni karo na 6 tsakanin kasashen Sin, Japan da kuma Koriya ta Kudu kuwa, Liu Zhenmin ya bayyana cewa, hadin kai a tsakanin kasashen uku muhimmin al'amari ne ga kokarin tabbatar da hadin kai tsakanin kasashen gabashin Asiya, kuma ana sa ran taron zai taka muhimmiyar rawa wajen inganta hadin kai a nahiyar Asiya. Ta la'akari da yanayin da ake ciki na fama da koma bayan tattalin arzikin duniya, ana gudanar da taron duk shekaru uku uku da nufin karfafa hadin kai da tabbatar da zaman lafiya a nahiyar Asiya, da kuma inganta bunkasuwar tattalin arzikin nahiya Asiya har da ta duniya baki daya. (Bilkisu)