in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya isa kasar Koriya ta kudu
2015-10-31 13:42:03 cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya sauka a kasar Koriya ta kudu domin fara ziyarar aiki a safiyar Asabar din nan 31 ga wata, sannan kuma zai halarci taron tattaunawar hadin gwiwwa tsakanin kasashen Japan, Koriya ta Kudu da kasar Sin karo na 6.

Ana sa ran a lokacin ziyarar, firaministan na Sin Li Keqiang zai gana da shugabar kasar Koriyan ta Kudu Madam Park Geun-hye da sauran manyan jami'an gwamnatin kasar, sannan ya halarci ayyukan hadin gwiwwa kan tattalin arziki da na musanyar al'ummomi.

A lokacin taron tattaunawa tsakanin Sin, Japan da Koriya ta Kudu da za'a yi bayan tsaikon shekaru uku da rabi, ana sa ran shugabannin kasashen uku su yi musanyar ra'ayi kan hadin gwiwwa da kuma batutuwan da suke jawo hankalin yankunansu da ma sauran duniya baki daya. Haka kuma za su halarci taron tattaunawa na kasuwanci. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China