Gilbert Diendere dai tun da farko ya nemi mafaka ne a gidan wakilin Vatican a kasar wanda daga baya aka kama shi bayan da sojojin dake biyayya ga gwamnati suka kai harin da ba na zubar da jini ba a manyan wuraren da sojojin rukunin juyin mulkin suke da karfi, sannan komai ya koma yadda ya kamata bisa kundin tsarin mulki a kasar dake yammacin Afrika.
Birgediya janar Gilbert Diendere dai an ce an mika shi hannun gwamnati domin ya amsa laifinsa.
Jagoran juyin mulkin ya ce damuwar shi kadai shi ne game da tsaron shi da na iyalin shi saboda yunkurin juyin mulkin ya samu suka daga daukan al'ummar kasar tare da kawo tashin hankali har wassu sun rasa rayukan su wadansu kuma kusan 200 suka jikkata.
A cewar majiyar soji fiye da rabin bangaren sojojin fadar shugaban kasar da aka rusa wato RSP, da rukunin sojoji na musamman 1300 da suka yi yunkurin juyin mulkin sun mika wuya kuma har yanzu suna kan mikawa. (Fatimah Jibril)