A cikin wata sanarwar gwamnati da aka fitar, an tabbatar da cewa, an riga an fara zaman sauraron shari'arsu, sannan kuma ana bincike da tambayoyi har ma da binciken gidajen wadanda ake zargi.
Janar Diendere wanda ya shirya yunkurin juyin mulkin a ranar 17 ga watan Satumba a kan gwamnatin wucin gadi kuma daga baya ya nemi mafaka a gidan ofishin jakadancin Vatican dake kasar a Ouagadougou, an mika shi ga hukumomi domin ya amsa laifin shi.
Tsohon babban hafsan sojin kasar a lokacin mulkin Blaise Campore wanda aka hambarar a watan Oktoban bara ya yi alkawarion mika kanshi ga muhukunta domin amsa laifin shi game da yunkurin juyin mulkin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 11 sannan wadansu 200 suka jikkata. (Fatimah Jibril)