A cikin wata sanarwa da Diendere ya bayar a wannan rana, ya ce, idan sojojin da ke goyon bayan gwamnatin wucin gadi suka kai musu hari, su ma za su kare kansu. A sa'i daya kuma, ya ce, yana jiran sakamakon da aka cimma a taron gaggawa da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ta shirya a birnin Abuja na tarayyar Nijeriya game da daftarin shiri da bangarorin daban daban na kasar suka daddale.
A ranar 20 ga wata, kungiyar shiga tsakani ta ECOWAS da wakilan zaratan sojojin da ke gadin fadar shugaban kasar Burkina Faso suka cimma ra'ayi guda game da daftarin shiri a birnin Ouagadougon da ke kasar, don kawo karshen tashe-tashen hankali, da yin afuwa ga sojojin da suka shirya juyin mulkin, kana za a mika mulki ga gwamnatin wucin gadin kasar, gami da shirya zaben majalisar dokoki da babban zaben kasar a ranar 22 ga watan Nuwamba.
Rahotanni na cewa, an kai shugaban wucin gadin kasar Michael Kafando da sojojin da suka shirya juyin mulkin zuwa ofishin jakadancin kasar Faransa dake kasar.(Bako)