Yace tun daga ranar Alhamis gwamnatin wucin gadin zai cigaba da aiwatar da ayyukan shi yadda ya kamata.
Kagfando wanda yake cikin wadanda aka kame a makon jiya lokacin juyin mulkin kafin a sako shi ya gode ma al'ummar kasar wadanda suka tabbatar da ganin yunkurin juyin mulkin da rundunar tsaron shugaban kasar suka yi na makon jiya yaci tura.
A daren tarlatan jiya ne bangaren sojojin da suka yi yunkurin juyin mulkin dana bangaren masu biyayya da gwamnati wadanda ke barazanar mai da martani tsakani suka rattaba hannu akan yarjejeniyar kawo karshen duk wata barazana da suke ma junan su.