Bisa labarin da aka samu daga rundunar sojan kasar Syria, an ce, Syria sun fara kai farmaki a birnin Aleppo dake arewacin kasar a ranar Jumma'a 16 ga wata, ya zuwa yanzu, sun riga sun sami iko kan wasu garuruwan dake kudancin birnin .
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha, kana wakilin musamman na shugaban kasar kan harkokin yankin Gabas ta tsakiya Mikhail Bogdanov ya bayyana cewa, ya kamata bangarorin kasa da kasa, shiyya-shiyya da kuma na kasar Syria su hada kai wajen yaki da 'yan ta'adda dake kasar Syria.
Bugu da kari, ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta fidda wata sanarwa a jiya Jumma'a cewa, Mikhail Bogdanov ya gana da jakadan kasar Syria dake kasar Rasha Riad Haddad a wannan rana, inda suka yi musayar ra'ayi kan halin da kasar Syria take ciki a halin yanzu.
Haka kuma a lokacin tattaunarwa, sun cimma matsayi daya cewa, ya kamata bangarorin kasa da kasa da kuma shiyya-shiyya da na kasar Syria su yi hadin gwiwa wajen yaki da 'yan ta'addan dake kasar Syria. (Maryam)