in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar shugaba Xi Jinping za ta karfafa hadin gwiwar hada-hadar kudi a tsakanin Sin da Birtaniya
2015-10-21 14:40:49 cri
Game da ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a kasar Birtaniya, shugaban garin hada-hadar kudi na birnin London Alan Yarrow ya bayar da sharhi, inda ya bayyana cewa, kasar Sin tana ci gaba da takawa hanyar kasancewa kasa ta zamani da raya tattalin arziki bisa tsarin bai daya a duniya. Kana ana shiga lokaci mai kyau wajen raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da samun bunkasuwa da wadata tare. Haka kuma Alan Yarrow yana hangen makoma mai kyau na hadin gwiwar hada-hadar kudi da tattalin arziki da cinikaya a tsakanin Sin da Birtaniya.

A ranar talata 20 ga wata, Mr Yarrow ya bayyanawa 'yan jarida cewa, yana begen ziyarar shugaba Xi Jinping a garin hada-hadar kudi na birnin London, a cewar shi, ziyarar tana da muhimmanci sosai wajen sa kaimi ga inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Birtaniya. Har ila yau shugaban garin ya bayyana cewa, a yayin ziyarar Shugaban kasar ta Sin, kasashen biyu za su samu sakamako da dama kan hadin gwiwarsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya da hada-hadar kudi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China