Sarauniya Elizabeth II ta bayyana a cikin jawabinta cewa, shekarar bana shekara ta musamman ce ga dangantakar dake tsakanin Birtaniya da Sin, tare da hadin gwiwa da sada zumunta a tsakaninsu. Ziyarar shugaba Xi Jinping a kasar Birtaniya tana da babbar ma'ana, wadda ta sa kaimi ga raya dangantakar sada zumunta a tsakaninsu.
Shi ma a nashi jawabin Shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, a matsayin kasar kawancen yaki da Fascist a yakin duniya na biyu, jama'ar kasashen Sin da Biryaniya sun nuna goyon baya da juna. A matsayin kasashen farko da kafa MDD da kasashen kwamitin sulhun MDD na dindindin, kasashen biyu suna daukar alhakin sa kaimi ga samun zaman lafiya da bunkasuwa a duniya tare. Ana bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, wanda zai amfanawa kasashen biyu har ma ga dukkan duniya gaba daya.
Tawagar Shugaba Xi da suka hada da Wang Huning, Li Zhanshu, Yang Jiechi tare da firaministan kasar Birtaniya David Cameron da shugaban jam'iyyar kwadago ta kasar Birtaniya Jeremy Corbyn sun halarci liyafar. (Zainab)