in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya mika sakon ta'aziyya ga takwaransa na kasar Benin game da rasuwar tsohon shugaban kasar
2015-10-21 12:14:33 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon ta'aziyya ga takwaransa na kasar Benin Boni Yayi game da rasuwar tsohon shugaban kasar Mathieu Kérékou a ranar 19 ga wata, inda ya nuna babban juyayi kan wannan rashi na shugaba Kerekou, tare da janjanta wa dangoginshi.

A cikin sakon, shugaba Xi ya ce, Kerekou babban abokin jama'ar kasar Sin ne, wanda ya ba da babbar gudummawa wajen raya dangantakar hadin gwiwa da sada zumunta a tsakanin kasashen biyu.

Shugaban Xi ya ce, Sin na dora muhimmanci sosai kan alakarta da Benin, kuma tana fatan yin kokari tare da kasar Benin, don cigaba da karfafa dangantakar hadin gwiwa da sada zumunta a tsakaninsu daga duk fannoni da kawo moriya ga kasashen biyu da jama'arsu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China