in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya yi jawabi a majalisar dokokin kasar Birtaniya
2015-10-21 08:35:37 cri

A ranar 20 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi jawabi a majalisar dokokin kasar Birtaniya, inda ya jaddada cewa, kamata ya yi kasashen Sin da Birtaniya su kara yin mu'amala da koyi da juna. Haka kuma su fahimci juna tare da nuna goyon baya da sada zumunta tsakanin su don inganta hadin gwiwar su zuwa wani sabon matsayi.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kasar Birtaniya ce ta farko da ta nemi kafa tsarin majalisar dokoki a duniya. A halin yanzu, jama'ar kasar Sin suna kokarin raya kasa bisa dokoki domin majalissun kasashen biyu su iya kara yin mu'amala da koyi fasahohi da juna.

Shugaban na Sin ya jaddada cewa, ko da yake akwai nisa a tsakanin Sin da Birtaniya, amma suna jawo hankulan juna cikin dogon lokaci. Tun bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin a shekarar 1949, huldar dake tsakanin kasashen biyu ta samu babban ci gaba a fannoni daban daban wadda ba a taba ganin irinta a tarihi ba.

Ya kara da cewa, Birtaniya kasa ce ta farko a yammacin duniya da ta amince da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, baya ga kyakkyawan jagoranci wajen kafa dangantakar daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashe membobin kungiyar EU. Sa'an nan Birtaniya tana kan gaba wajen musayar kudin RMB bayan yankin HongKong, baya ga yadda ta zama kasar da ta fi jawo yawan dalibai Sinawa tare da kafa kwalejin Confucius mafi yawa a cikin kasashe membobin kungiyar EU. Har ila yau ita ce kasa ta farko a yankin Turai da ta yi amfani da kudin RMB wajen samar da rance, sannan ta zama kasa ta farko a yammacin duniya wajen neman shiga bankin zuba jari kan muhimman ababen more rayuwa a nahiyar Asiya. Duk wadannan abubuwa sun tabbatar da cewa, Sin da Birtaniya na cikin yanayi na cin moriya juna.

Shugabar majalisar dattijai ta kasar Birtaniya Baroness Frances D'Souza ta yi jawabi tare da nuna godiya ga shugaba Xi Jinping a kan ziyarar da ya kai a majalisar dokokin kasar.

Firaministan kasar Birtaniya David Cameron, membobin majalisar dattijai da ta wakilai, wakilan sarauniyar kasar, ministocin gwamnatin kasar, manyan jami'an gwamnati da majalisar dokokin kasar gaba dayan su suka halarci zaman majalisar a wannan rana. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China