in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na da makoma mai kyau ta fuskar kirkire-kirkire, in ji wakilin kasuwancin kasar Birtaniya
2015-10-20 15:35:43 cri

A jajibirin kai ziyarar aiki a kasar Birtaniya da shugaba Xi Jinping na kasar Sin zai yi, Ron Dannis, shugaban kamfanin McLaren, kuma babban daraktan zartaswa na kamfanin, kuma mutumin da Firaiministan Burtaniya David Cameron‎ ya nada a matsayin wakilinsa a fannin kasuwanci, ya zanta da wakilinmu na CRI, inda ya bayyyana cewa, ziyarar aikin mista Xi zuwa Birtaniya ta zama wata muhimmiyar dama ga shugabannin kasashen biyu wajen kara fahimtar juna da amincewar juna.

Yanzu ga karin bayanin daga abokiyar aikinmu Bilkisu.

Kungiyar McLaren tana daya daga cikin kungiyoyin tseren motoci na F1 da suka fi samu maki mai kyau. A matsayinsa na shugaban kamfanin, kuma babban daraktan zartaswa na kamfanin, 'yan kasuwa da dama na kasar Sin sun san wannan suna na Ron Dannis. A shekarar 2014 ne firaministan Birtaniya David Cameron ya nada shi a matsayin wakilin kasuwanci a fannonin masana'antu da wasu manyan ayyuka na kasar. A yayin da yake ambatar ziyarar shugaba Xi Jinping a kasarsa, Dannis ya bayyana cewa, a wasu lokuta kwarya-kwaryar tattaunawa ta fi wasu shawarwari na gwamnati wajen inganta yin mu'amala tsakanin bangarori biyu.

"A ganina, abin da ya fi muhimmanci kan wannan ziyarar aiki shi ne, ba wai iya tattauna muhimman ayyukan hadin kai kawai ba, har ma da kara fahimtar juna da amincewar juna. Kamar yadda mu kan yi a zaman rayuwarmu, idan mun gamu da matsala, za mu nemi taimako daga abokanmu, hakan na nuna amincewa da fahimtar juna na da muhimmanci sosai wajen gudanar da hadin kai tsakanin kasa da kasa. Ziyarar da shugaba Xi zai yi a kasar Birtaniya wata dama ce mai kyau wajen kara fahimtar juna da amincewar juna tsakanin kasashen biyu. A ganina, za a dora muhimmanci sosai kan tattaunawar da shugabannin biyu za su yi a gidan firaminista Cameron na Chequers, irin yanayin tattaunawar zai taimaka wa bangarorin biyu wajen kara fahimtar juna."

Bayan haka kuma, Ron Dannis ya ce, yin kirkire-kirkire zai inganta bunkasuwar kamfanoni, yana fatan 'yan kasuwan kasar Sin na kokarin yin kirkire-kirkire, don samun makoma mai kyau a nan gaba, saboda haka ne ya nuna goyon baya ga ministan kudi na kasar Birtaniya George Osborne kan shirinsa na mayar da kasar Birtaniya a matsayin babbar kawa ga kasar Sin a kasashen yammacin duniya.

"Har zuwa yanzu kasashe da yawa suna daukar wani tsohon ra'ayi, suna tsamanin kasar Sin na iya samar da 'yan kwadago masu araha kawai. Amma, duk wanda ke tafiya a kasar Sin a kullum kamar yadda nake, sun fahimci cewa, wannan ra'ayi ya tsufa. Yanzu haka ana iya ganin ayyukan muhimman kayayyakin more rayuwa na zamani a kasar Sin, kuma ana gudanar da wadannan ayyuka cikin sauri, abin da ya fi muhimmanci shi ne, suna amfani da fasahohin zamani na duniya."

A shekarar 2014, Ron Dannis da wasu shugabannin manyan kamfanonin kasa da kasa na Birtaniya sun kafa kwamitin kula da harkokin gabashin Asiya na Birtaniya, da nufin inganta harkokin diplomasiyya tsakanin shugabannin kasashen Sin da Birtaniya, da ciyar da hadin kai tsakanin bangarorin biyu a fannonin cinikayya da al'adu gaba. A matsayinsa na shugaban kwamitin, Dannis yana ganin cewa, neman moriyar bai daya bisa manyan tsare-tsare muhimmin sashe ne na ingantan dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Birtaniya, ya kara da cewa, shirin da kasarsa ke tsarawa na zirin tattalin arziki a arewacin Ingila, da shirin tattalin arziki da kasar Sin ta gabatar na "Zirin daya da hanya daya" sun kasance wani abun dake iya karfafa hadin kai a tsakanin kasashen biyu..

"Manufofin biyu suna bukatar juna. Ba kawai ya nuna cewa shugabannin kasashen biyu suna da basira ba, har ma ya nuna wata alama cewa, hadin kai a tsakanin kasashen Sin da Birtaniya zai yadu daga fannin gudanar da ayyuka zuwa more fasahohin sadarwa."

A bisa tsare tsaren da aka yi, a yayin ziyararsa a Birtaniya, shugaba Xi zai kai ziyara a sashen nazarin ilmin sinadarin Graphene a jami'ar Manchester. Game da haka Dannis ya ce, kasarsa na da fasahohin zamani dangane da nazarin sinadarai, a nata bangare kasar Sin na da kwarewa wajen kire-kire, saboda haka idan bangarorin biyu suka hada kai a fannin, to za a iya bunkasa kasuwar sinadarai cikin nasara. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China