in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu fasahohin al'adu na Birtaniya sun yi kira ga jama'ar kasar da su kara kokarin sanin kasar Sin
2015-10-19 13:40:58 cri

A yau Litinin shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fara ziyararsa ta yini 5 zuwa Birtaniya, ziyarar wadda ke da ma'ana sosai a fannonin siyasa da cinikayya da kuma raya al'adu.

A nan kasar Sin, William Shakespeare, tare da sarauniya Elisabeth da David Beckham, sun kasance shahararrun 'yan Birtaniya da Sinawa suka fi fahimtar tarihinsu. Da yawa daga cikin jama'ar kasar Sin da muka yi hira da su, sun taba karanta littattafan wasannin kwaikwayon da Shakespeare ya rubuta, har ma sun rike wasu muhimman darrusa daga cikin littattafan.

A watan Yulin bana, kamfanin wasan kwaikwayo na kasar Sin NTCC, wato "National Theatre Company of China" a Turance, ya nuna wani wasan kwaikwayo mai taken "Sarki Richard na Uku", wanda Shakespeare ya tsara, a birnin London, ta yadda aka kaddamar da bikin nuna al'adun kasar Sin, karkashin laimar shekarar musayar al'adu tsakanin Sin da Birtaniya ta 2015. Game da wasan kwaikwayon da aka nuna ta yaren Sinanci, Chatherine Mallyon, babbar darektar dakin nuna wasannin kwaikwayo na Royal Shakespeare Theatre na kasar Birtaniya, ta ce wasan ya burge ta kwarai da gaske.

"Wasan ya sa ni jin dadi, kuma ya burge ni matuka. Kun san jama'a suna cewa, Shakespeare na duk duniya ne, domin abubuwan da ya rubuta suna cikin al'adun duniya masu muhimmanci. Sa'an nan 'Sarkin Richard na Uku' da aka nuna da Sinanci ya nuna yadda Shakespeare ya zama na jama'ar duniya ke nan."

Ita Chatherine Mallyon ta kasance cikin wata tawagar jami'an gwamnatin kasar Birtaniya, wadda ta kai ziyara kasar Sin a watan Satumba da ya wuce, don haka ta samu damar gane wa idon ta yadda ake samun sakamako sosai ta fuskar hadin gwiwar Sin da Birtaniya, musamman ma a fannonin al'adu da cinikayya. A ganinta, ziyarar shugaba Xi Jinping a kasar Birtaniya, za ta kara samar da yanayi mai kyau ga cudanyar kasashen 2 a fannin al'adu.

"Na yi amana cewar, yana da muhimmanci sosai yadda Birtaniya da Sin su ke cigaba da musayar ra'ayi a fannin al'adu. Ya kamata mu yi kokarin fahimtar ra'ayin junanmu dangane da al'adu, domin hakan zai taimaka mana samun fahimta a tsakaninmu. A ganina, shugabannin kasar Sin su ma suna dauke da wannan ra'ayi."

A nashi bangare, Rana Mitter, darektan cibiyar nazarin kasar Sin ta jami'ar Oxford, shi ma yana mai da hankali sosai kan ziyarar shugaba Xi Jinping a kasar Birtaniya. A ganinsa, har yanzu jama'ar kasar Birtaniya ba su fahimci kasar Sin sosai ba.

"Ina fatan ganin ziyarar shugaba Xi Jinping za ta sanya jama'ar kasar Birtaniya fahimtar muhimmiyar rawar da kasar Sin ke takawa a fannoni daban daban, gami da sanya su su yi kokarin kara sanin kasar Sin. Saboda a ganina jama'a ba su fahimci kasar Sin sosai ba, duk da cewa sun san kasar tana samun cigaba sosai a fannin tattalin arziki, amma ba su fahimce ta ba ta fuskar sauran bangarori. Don haka, ina fata ziyarar da firaminista da ministan kudi na kasar Birtaniya suka yi a kasar Sin, gami da ziyarar shugaban kasar Sin a Birtaniya a wannan karo, dukkansu za su taimakawa alummar Birtaniya fahimtar kasar Sin sosai."

Bugu da kari, a cewar Mista Mitter, yanzu a Birtaniya ana kara ba da muhimmanci kan nazarin al'adun kasar Sin, gami da tarihin kasar. Dalilin haka ne ya sa aka kaddamar da cibiyar nazarin kasar Sin a jami'ar Oxford a watan Satumbar bara. Ban da haka kuma, cikin shekaru 10 da suka wuce, an kafa sassan nazarin kasar Sin a jami'o'in kasar Birtaniya da yawa, kamarsu jami'ar Manchester da jami'ar Southampton da jami'ar Warwick da dai sauransu. A ganin Rana Mitter, akwai karin 'yan Birtaniya da suka yi sha'awa ga nazarin tarihi da al'adun kasar Sin, musamman ma tsakanin matasan kasar.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China