in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Magatakardar MDD yayi tir da kisan ma'aikatan wanzar da zaman lafiya a jamhuriyar CAR
2015-10-08 10:26:16 cri
Magatakardar MDD Ban Ki-Moon yayi tir da hallaka ma'aikacin wanzar da zaman lafiya da aka yi a jamhuriyar Afrika ta tsakiya tare da kiran da a tabbatar da an yi hukuncin wannan danyen aiki.

Magatakardar yayi suka da babbar murya a kan harin da ake kai ma ma'aikatan kiyayen zaman lafiya na MDD, tare da kiran da a dauki matakin gaggawaa wajen gurfanar da masu laifin gaban kuliya.

Kamar yadda kakakin majalissar Stephen Dujjaric ya bayyana cikin wata sanarwa, wadansu da ba'a san ko su wanene ba suka kai ma ayarin ma'aikatan majalissar hari a kan hanya mai tazaran kilomita 55 a arewacin Bangui babban birnin kasar a ranar talata.

Sojoji masu tsaron ayarin motocin su ma nan take suka maida martani ta hanyar bude wuta inda a ranagamar ma'aikaci daya ya mutu sannan daya kuma ya ji rauni.

Magatakardar MDD ya bukaci kungiyoyin dake dauke da makamai a kasar da su kawo karshen fadan da suke yi tare da mika makaman su. Ya kuma jaddada aniyar majalissar na taimakawa muhukuntar kasar a yakin da suke yi akan ta'addanci da kuma son ganin an kawo karshen tashin tashina.

Steven Dujjaric ya ce ofishin Majalissar ta kara kokarin da take yi na sintiri a kusa da ofishin wucin gadin kasar. Baya ga babban birnin kasar, ma'aikatan wanzar da zaman lafiya na cigaba da sa ido a duk wani kai komo da kungiyoyi masu dauke da makamai ke yi a wurare daban daban na kasar.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China