in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta nada shugaban tawagar wanzar da zaman lafiya a jamhuriyar demokaradiyyar Congo
2015-10-09 11:07:29 cri
Babbabn sakataren MDD Ban Ki Moon ya nada Maman S. Sidikou daga jamhuriyar Nijar a matsayin shugaban tawagar MDD mai aikin wanzar da zaman lafiya a jamhuriyar demokaradiyyar Congo wato MONUSCO a takaice.

Mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric, ya bayyana cewar bayan wancan mukamin, MDD ta nada shi Mista Siddiko a matsayin babban sakaren tawagar wakilan MDD a jamhuriyar demokaradiyyar Congo wanda zai maye gurbin Martin Kobler dan kasar Jamus.

Mista Ban, ya godewa Kobler saboda gagarumar gudunmowar da ya bayar wajen aiwatar da manufofin MONUSCO wanda ya shafe shekaru 2 yana jagoranta.

Dujarric ya ce, shi dai Mista Sidikou, ya shafe sama da shekaru 25 yana aiki da MDD a bangarori daban daban da kuma kungiyar hada kan kasashen Afrika AU.

Kafin nada shi a wannan mukami Sidikou, ya kasance wakili na musamman ga kungiyar AU a kasar Somaliya, kuma yana rike da shugabancin tawagar wanzar da zaman lafiya na kungiyar AU a Somali wato AMISOM.

Sadikou ya rike mukumai da dama a kasar sa tun daga shekarar 1976, mukami na baya bayan nan shi ne jakadan jamhuriyar Nijar a kasar Amurka tsakanin shekarar 2011 zuwa 2014, yayi karatunsa na digirin digirgir a jami'ar jahar Florida ta kasar Amurka a fannin Ilmi, yana da mata da yara 2. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China