Wani jami'in bangaren soja na kasar Syria ya bayyana wa 'yan jarida cewa, wannan ne karo na farko da sojojin gwamnatin kasar suka dauki matakin soja a karkashin taimakon sojojin sama na kasar Rasha kan garuruka biyu dake karkara ta arewacin jihar Hama wadanda dakarun kawancen masu adawa suka mallaka, burinsu shi ne mallake hanyoyin dake tsakanin jihar Hama da ta Homs.
Bisa sanarwar da ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta bayar a ranar Laraba, an ce, bangaren sojin kasar Rasha ya tura jiragen saman yaki don lalata wurare da dama dake karkashin mallakar kungiyar IS.
Sojojin saman kasar Rasha sun fara taimakawa sojojin kasar Syria wajen kai harin sama ga wuraren kungiyar IS tun daga ranar 30 ga watan Satumba. Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad ya amince tare da nuna yabo ga harin sama da sojojin saman kasar Rasha suka kai a hirar shi da manema labarai na kasar Iran a kwanakin baya. (Zainab)