Sojojin kasar Isra'ila sun bayyana a cikin wata sanarwa cewa, a ranar 20 ga wata, an kai hari da makaman roka guda 4 ga arewacin kasar Isra'ila dake dab da kan iyakar kasar da Syria, ko da ya ke harin bai haddasa mutuwa ko raunatar mutum ko daya ba.
Amma Isra'ila na zargin kungiyar masu ra'ayin Jahadin Islama, da gwamnatin kasar Syria da ta kasar Iran suke mata goyon baya, ta kai wannan hari, kana ta bukaci gwamnatin kasar Syria da ta dauki alhakin kai harin. Ya zuwa yanzu, ba a san ko akwai 'yan kasar Syria da suka mutu ko raunata a sakamakon harin sojojin Isra'ila ba.
Hakazalika kuma, sojojin kasar Isra'ila sun girke na'urorin kakkabo makaman roka a birnin Ashdod da Beer Sheva dake kudancin kasar don magance yiwuwar tsanantar halin da ake ciki a sakamakon shakkun tunanin mutuwar wani Bafalesdine da ake tsare da shi a zirin Gaza saboda kin cin abinci da ya yi na tsawon lokaci. (Zainab)