in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta samar wa Syria da wasu kasashe taimakon jin kai na RMB yuan miliyan 100
2015-10-16 19:20:29 cri
A ran Jumma'an nan 16 ga wata, ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta sanar da cewa, domin taimaka wa kasar Syria da sauran kasashen kewaye dake fama da matsalar 'yan gudun hijira wajen fuskantar da matsalar jin kai mai tsanani, gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin samarwa kasashen Syria, Jordan, Lebanon da dai sauran kasashe taimakon jin kai na kudin Sin RMB yuan miliyan dari daya.

Haka kuma, a yayin da yake ganawa da takwaransa na kasar Croatia, Kolinda Garbar Kitarovic a ranar Laraba 14 ga wata, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin tana mai da hankali kan batun 'yan gudun hijira da ya faru a Turai da bahar Rum. Haka kuma Sin na tausaya ma kasashen da matsalar ta shafa. Ya ce adon haka ya sa gwamnatin kasar Sin za ta samar wa kasashen da abin ya shafa taimakon kudin jin kai, domin sassauta matsalolin jin kai da kasashen ke fama da su a halin yanzu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China