in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hari ta jiragen saman yaki ya hallaka mutane 58 a yankin da 'yan tawaye ke rike da shi kusa da Damascus
2015-08-17 09:44:58 cri

Rahotanni da kasar Sham ya tabbatar da cewar, harin jiragen saman yakin kasar ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 58 sannan fiye da 200 suka jikkata a wani yankin da 'yan tawaye ke rike da shi daga gabashin birnin Damascus a ranar Lahadin nan.

Jiragen saman yakin kasar dai sun jefa makamai masu linzami sau da dama a wajen garin Douma dake gabashin birnin Damascus kamar yadda wata kungiya mai sa ido kan hakkin bil Adama ta tabbata. Kungiyar ta kuma ce, adadin wadanda suka mutu na iya karuwa saboda yawan wadanda suka ji rauni.

Wannan hari ya kuma jawo asarar kayayyaki a birnin na Douma, babban garin da kungiyar Jaish al-islam ko kuma sojojin musulunci ke da sansani a gabashin Ghouta na wajen birnin Damascus.

Wadansu makaman masu linzami sun fada a cikin kasuwanni a wannan wajen, in ji kungiyar lura da hakkin bil adama ta kasar Ingila.

A wani bangaren kuma kamfanin dillanci labarai na kasar SANA ta ce, sojojin sama na kasar sun kai harin ne a kan sansanonin 'yan ta'adda a gabashin Ghouta, inda suka lalata makaman roka, sansanonin makamai tare da hallaka 'yan ta'addan da dama galibin su 'yan kasashen waje.

A daukacin lokacin da kasar ke fama da tashin hankali, Douma ta kasance wani jigon kungiyoyin masu kaifin addini a gabashin Damascus musamman sojojin musulunci.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China