Kaza lika, babbar sakatariyar hukumar kula da ilmi, kimiyya da al'ada ta MDD wato UNESCO Irina Gergieva Bokova da shugabar kasar Mauritius kana masaniya a fannin kimiyyar halittu Ameenah Gurib-Fakim da wasu shugabannin mata a fannoni siyasa, ciniki da kimiyya da fasaha sama da dari daya ne suka halarci taron, tare da yin musayar ra'ayoyi kan yadda za a raya tattalin arziki, tabbatar da zaman daidai wa daida a tsakanin maza da mata da sauran harkoki. (Maryam)