A yayin taron manema labaru da aka shirya a yau, kakakin ofishin yada labaru na majalisar gudanarwar Sin Hu Kaihong ya bayyana cewar, takardar bayanin ta kunshi alkaluma da abubuwan da ke faruwa a kasar, kana an nuna matakan da Sin ta dauka wajen samar da daidaito tsakanin bambancin jinsi da raya harkokin mata, da ma ci gaban da aka samu a kasar.
Mr. Hu ya ce, wannan ya kasance takardar bayani na uku da gwamnatin Sin ta fidda wajen raya harkokin mata, kuma an fidda takardu da harsunan Sinanci da Turanci da Faransanci da Rashanci da Jamusanci da Larabci da kuma harsunan Spaniya da Japan.(Bako)