Hong Lei wanda ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai game da taron shugabannin kasashen duniya kan samar da daidaiton tsakanin jinsi da 'yancin mata, taron da ya gudana jiya Lahadi a hedkwatar MDD, Ya kuma bayyana irin gudummawar da kasar Sin ta bayar game da harkokin da suka shafi ci gaban mata.
Yayin taron shugaba Xi ya kuma gabatar da wasu shawarwari guda 4 game da 'yancin mata. Na farko ya ce, dole ne a mai da hankali kan 'yancin mata ta hanyar ba su damar shiga harkokin ci gaban zamantakewar al'umma da tattalin arziki. Na biyu, wajibi ne a martaba mata kana a bullo da dokokin da za su tabbatar da kare musu hakkokinsu.
Na uku, wajibi ne a kawar da duk wasu nau'o'in amfani da karfin tuwo kan mata. Na hudu kuma na karshe shi ne,a yi kokarin samar da yanayin ci gaban da ya dace ga mata.
Kimanin wakilai 100 da suka hada da shugabanni da gwamnatocin kasashe 80 ne suka halarci taron, inda suka bayyana kudurinsu na kawar da gibin da ke akwai tsakanin jinsi. (Ibrahim Yaya)