in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Rwanda ya yi kiran da a kawo karshen tashe-tashen hankali kan mata
2015-08-19 10:17:56 cri

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya yi kira da a kara daukar kwararrun matakai domin kawar da tashe-tashen hankalin da mata suke fuskanta, matsalolin dake karuwa a fadin duniya duk da kokarin da ake na kafa dokoki domin kare 'yancin mata.

Mista Kagame ya yi wannan kira a ranar Talata jim kadan bayan ya kaddamar da wani taron horar da jami'an tsaro na kasashen Afrika 30, mai taken "Hadin kan Afrika" a cibiyar 'yan sandan kasar Rwanda a unguwar Kacyiru, dake shiyyar Kigali, babban birnin kasar.

Zaman taron ya tattara mahalarta da za su samu tarin ilimi domin gano hanyoyin da za su taimaka wajen kawo karshen duk wasu ayyukan amfani da karfi ko tashe-tashen hankali kan mata da 'yan mata.

Gallazawar da ake yi wa mata da 'yan mata ta kasance abin da ba za a amince da shi ba a cikin al'ummomi domin wani hali ne na karya 'yancin dan adam, wani mugun laifi ne kana wata barazana ce ga cigaban Afrika da ma duniya baki daya. Ana bukatar kokarin hada kai domin kawo karshen wannan annoba da ta shafi duniya, in ji mista Mista Kagame.

Abin da aka kaddamar a cikin watan Febrairun shekarar 2008, Kamfen "Hadin kan Afrika domin kawo karshen tashe tashen hankali kan mata" na sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon, wani kamfe ne bisa tsawon shekaru masu zuwa dake manufar hana da kuma kawar tashe tashen hankali kan mata da 'yan mata a fadin duniya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China