Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya jagoranci bude taron dake neman shata wani sabon yunkuri na baiwa mata da 'yan mata 'yanci tafiyar da harkokin rayuwarsu a kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara.
Daya daga cikin manyan makasudai na ajandar shekarar 2063 na kungiyar tarayyar Afrika shi ne na aza daidaici jinsuna a matsayin ginshiki na ajandar neman bunkasuwa na nahiyar Afrika. An fi maida hankali kan muhimman fannoni biyar, wato kiwon lafiya, ilimi, tattalin arziki, noma, zaman lafiya da tsaro domin baiwa mata da 'yan mata 'yanci, in ji shugaba Kenyatta. (Maman Ada)