in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba za a iya warware matsalar 'yan gudun hijira ba illa a samu zaman lafiya da ci gaba
2015-10-14 20:10:00 cri

Kasashen Turai na ci gaba da fama da matsalar 'yan gudun hijira, inda miliyoyin 'yan gudun hijira daga kasar Sham da sauran kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da arewacin Afirka ke ci gaba da kwarara zuwa kasashen na Turai, kuma wannan matsala ce da kasashen da za su iya jure ta ba.

Wasu masana harkokin kasa da kasa na kasar Sin sun bayyana a kwanan baya cewa, matsalar 'yan gudun hijirar na da nasaba da yake-yaken da aka dade ana fama da su a wadannan yankuna. Don haka, sai an samu zaman lafiya da ci gaba kafin a kawo karshen wannan matsala baki dayan ta.

Yayin da suke zantawa da manema labaru, masanan sun ce, dole ne kasashen da ke yankin Gabas ta Tsakiya su sauke nauyin da ke kansu na magance matsalar rashin kwanciyar hankali a yankin, musamman ma batun matsalar 'yan gudun hijira, matsala ce da ke da nasaba da abubuwan da kasashen yammacin duniya, kamar Amurka suka aikata a yankin.

Har wa yau, masanan sun yi nuni da cewa, tsoma bakin kasashen waje, ba zai samar da kwanciyar hankali na zahiri ba. Haka kuma, tsari da tunanin kasashen yammacin duniya ba za su warware dukkan matsalolin da kasashen duniya ke fuskanta ba. Kamata ya yi al'ummar kowace kasa su tsara makomar kasarsu da kansu. Kuma ba wata kasar da za ta iya warware matsalar wata kasa daban, illa kowace kasa ta zabi hanyar raya kanta da ta dace da halin da take ciki. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China