in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan ci rani 34 suka mutu yayin jirgin ruwa ya nutse a tekun Aegean na Girka
2015-09-14 09:35:05 cri

A kalla 'yan ci rani da 'yan gudun hijira 34 da suka hada yara kanana 15 suka mutu, a yayin da wani jirgin ruwan dake dauke da su ya nutse a ranar Lahadi a tekun Aegean a yankin gabar ruwan tsibirin Farmakonissi a lokacin da suke kokarin shiga Turai, a cewar sojojin ruwan kasar Girka.

Wannan sabon bala'i ya tada hankalin Girka, da ta sake jaddada kiranta ga kungiyar tarayyar Turai da ta gaggauta daukar mataki da bullo da wani shiri domin daidaita matsalar kwararar 'yan ci ranin da ba su da takardu da kuma 'yan gudun hijira a wannan shekara.

Bayan nutsewar wannan jirgin ruwan dake dauke da 'yan ci rani da 'yan gudun hijira da ba a tantance adadinsu ba daga kasar Turkiya zuwa kasar Girka, an kiyasta cewa, mutanen da suka tsirar da rayukansu dake cikin jirgin ruwan sun kai 100 zuwa 120, haka kuma sojojin ruwan Girka sun tsamo gawawwakin wadanda suka mutu. A cewar wasu bayanai na baya bayan nan, akwai jarirai hudu da kuma kananan yara goma sha daya daga cikin mutanen da suka mutu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China