Ya zuwa yanzu dai gwamnatin Nigeriya ta karbi 'yan kasarta da suka je gudun hijira a Kamaru sakamakon rikicin 'yan Boko Haram su 9,000 wadanda yawancinsu mata da yara ne, kamar yadda jami'in kula da sansani na hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar NEMA Alhaji Sa'ad Bello ya tabbatar wa manema labarai a jihar Adamawa.
Ya yi bayanin cewar, kwanan nan hukumar NEMA ta karbi wadansu mutanen 650 da aka dawo da su daga kasar ta Kamaru, abin da ya kai adadin 9000 ya zuwa yanzu.
Hukumar ta NEMA ta tsugunar da wadanda suka rasa muhallansu a sansanoni 4 a cikin jihar, kuma an yi masu cikakken bincike na tsaro da na kiwon lafiya, sannan ana kara shirin karbar wadansu da su ma suka rasa matsugunnan nasu da za su dawo daga Kamarun. (Fatimah)