Shugaban kungiyar tarayyar Turai wato EU Jean-Claude Juncker, ya bukaci mambobin kungiyar ta EU da su kasafta a tsakanin su bakin haure kimanin dubu 12 da suka isa kasashen Italiya da Girka da kuma Hungary bisa la'akari da tsarin dokokin kungiyar.
Juncker ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin taron kwamitin kungiyar EU a birnin Strasbourg yayin tattauna yadda za'a shawo kan matsalar bakin haure, wacce ke ci gaba da karuwa a kullum a nahiyar Turai.
Za dai a gudanar da kasafin ne karkashin tsauraran dokokin kungiyar, kuma bisa tsarin dokar, kasashen Jamus da Faransa su ne za su dauki kashi 46 cikin 100 daga cikin adadin bakin hauren dubu 12.
Sai dai batun rabon dubun dubatar bakin hauren ya haifar da zazzafar mahawara, inda wasu daga cikin mambobin kasashen ke sukar lamarin kudurin dokar dake nuna wajabcin karbar bakin hauren.
Bisa la'akari da yawan karuwar da ake samu na 'yan gudun hijirar, Juncker, ya ce, wajibi ne al'ummar nahiyar Turai su jajurce domin tallafawa wadanda wannan al'amari ya shafa.
Ana sa ran a ranar 14 ga wannan wata ne kwamitin EU za ta mika jadawalin kason bakin hauren ga taron gaggawa na wakilan ministocin kungiyar. (Ahamd Fagam)