in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin EU sun amince da kasafta 'yan gudun hijira dubu 120
2015-09-23 10:50:15 cri

Bayan kammala taron gaggawa a jiya Talata, ministocin kungiyar tarayyar Turai wato EU sun amince da rarraba 'yan gudun hijira kimanin dubu 120 a tsakanin mambobin kasashen.

Majalisar tabbatar da adalci da harkokin cikin gida ta kungiyar ta sanar a shafin ta na twitter cewar, ministocin mambobin na EU sun amince da kaso mafi rinjaye.

Kwamitin na EU ya gabatar da bukatar rarraba 'yan gudun hijirar ne bayan fuskatar karuwar su, hakan ta sa aka yi ta samun kiraye kirayen nema rarraba 'yan gudun hijirar karkashin dokokin wajabcin karbar adadin dubu 160 na 'yan gudun hijirar.

A ranar Litinin din nan ministocin kungiyar EU sun amince a karbi bakuncin 'yan gudun hijirar dubu 40 daga kasashen Italiya da Girka.

Sai dai batun ya haifar da zazzafar mahawara, inda kasashe da dama daga gabashi Turai, kamar su Hungary da Poland da Czech da Slovakia suka nanata adawar su ta tilastawa kasashen karbar 'yan gudun hijirar.

Shugaban kungiyar ta EU Jean-Claude Juncker tare da shugabannin kasashen Jamus da Faransa sun tsaya kai da fata domin ganin mambobin kasashen sun amince wajen mutunta dokokin kungiyar ta EU.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China