in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya bukaci shugabannin EU da su nuna dattaku a taron tattauna makomar 'yan gudun hijira
2015-09-22 10:59:13 cri

Babbban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bukaci shugabannin kungiyar tarayyar Turai wato EU da su nuna halin dattaku a babban taron da ake shirin gudanarwa domin tattauna batutuwan da suka shafi 'yan gudun hijira da bakin haure wadanda ke kauracewar gidajensu domin neman mafaka

Ban ya yi wannan kira ne a Litinin din nan a ta bakin mai magana da yawunsa, inda ya bayyana cewar, kasancewar shugabannin na EU za su hallara a yau Talata, kuma za'a gudanar da taron ne a gobe Laraba, ya bukace su da su jajurce domin tallafawa mutanen da suka kauracewa matsugunansu bisa la'akari da tanade tanaden dake kunshe a yarjejeniyar kungiyar kan batun 'yan gudun hijira.

Babban sakataren ya nuna damuwarsa saboda halin kuncin rayuwa da kuma fuskantar tashin hankali da 'yan gudun hijirar da rikici ya raba da matsugunan ke fuskanta, wadanda tuni suka tsallaka Turai don neman mafaka.

Ya ce, da yawa daga cikin mutanen suna fuskantar cin zarafi ne da shiga cikin mawuyacin hali, kuma suna bukatar daukin gaggawa, don haka Ban ya bukaci kasashen na Turai da su taimaka musu bisa tanade tanaden dokar, sannan ya koka dangane da rufe kan iyakokin da wasu kasashen na Turai suka yi da nufin hana 'yan gudun hijirar kwarara kasashen nasu, da rashin tanadar musu kayayyakin jin kai, a wasu lokutan har ma da cin zarafinsu ko keta musu haddi.

Shugaban kungiyar ta EU Donald Tusk ya kira taron kungiyar ne bayan bukatar da shugabar Jamus Angela Merkel ta gabatar masa wato a gudanar da taron domin rarraba 'yan gudun hijirara a tsakanin mambobin kasashen, saboda kasashen Jamus da Sweden na samun karuwar sabbin 'yan gudun hirarar a ko da yaushe.

A ranar 30 ga watan Satumba, babban sakataren na MDD zai gudanar da wani taron na musamman domin tattauna irin kalubalen da kasashen duniya ke fuskanta sakamakon karuwar 'yan gudun hijira.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China